An sake saka ranar ci gaba da sauraren shari'ar Ganduje kan shugabancin APC


Kotun tarayya ta sake saka ranar da za ta cigaba da sauraren karar da aka shigar da shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje 

Babbar Kotun tarayya da ke ta sake saka 26 ga wannan watan na Yuni, 2024 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraren karar da 'yan yankin arewa ta tsakiya suka shigar da ke neman a cire Abdullahi Umar Ganduje a Sha jam'iyyar APC ta kasa.

'Yan yankin na arewa ta tsakiya dai na neman a cire Ganduje a ba su shugabancin jam'iyyar kasancewar kamar yadda suka ce, gurbin na yankin ne, bayan da Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukamin.

Post a Comment

Previous Post Next Post