Sarki Aminu ya nemi karin jami'ai na musamman daga 'yan sandan Kano


Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya samar da tsaro na musamman gabanin bukukuwan Sallah Babba.

Bukatar hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike ma kwamishinan yan sandan jihar, mai dauke da kwanan watan 10 ga Yuni 2024.

A cewar wasikar Sarkin ya gode wa ‘yan sanda kan tabbatar da zaman lafiya a jihar biyo bayan rikicin da ya biyo bayan dawo da Sarki Sanusi Lamido kan karagar mulki.

Post a Comment

Previous Post Next Post