Har yanzu bamu cimma matsaya ba kan mafi karancin albashi a Nijeriya - kungiyar kwadago


Kungiyoyin Kwadago sun yi watsi da ikirarin shugaban kasa Bola Tinubu na cewa an cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaba Tinubu ya yi ikirarin cewa an cimma matsayar ne kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana ja-in-ja tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a kasar.

A jawabinsa na bikin ranar dimokuradiyya a wannan shekarar ta 2024 da ya gudana a Abuja ranar Laraba, Tinubu ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka ga majalisar dokokin kasar domin ta amince da mafi karancin albashi.

Shugaban ya jaddada cewa gwamnatinsa ta zabi tsarin dimokuradiyya wajen magance bukatun kungiyoyin kwadago a kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post