'Yan bindiga sun hallaka mutane kusan 30 a wani sabon hari a kauyen Katsina


'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Kunamawa na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina a ranar Laraba.

Harin kamar yadda majiyar DCL Hausa ta sanar ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 27 tare da raunata masu yawa.

Bayanai sun ce maharan sun je kauyen ne da yammaci, inda suka bude wuta su na harbin kan mai uwa da wabi kan mutanen gari, suka kashe masu karar kwana suka raunata masu tsautsayi kamar yadda majiyar ta tabbatar.

Kauyen Kunamawa bai fi nisan kilomita 10 ba daga hedikwatar karamar hukumar Safana ta jihar Katsina. 

Wata majiyar ta ce mutanen da suka rasu, sun kai 30, a yayin da wadanda suka samu raunuka suke kwance a asibiti karkashin kulawar likitoci.

Wasu bayanan sun ce matasan yankin sun gudanar da wata kwarya-kwaryar zanga-zanga don neman agajin hukumomi kan yawaitar hare-haren tun bayan saukar ruwan sama.

Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, babu wata sanarwa a hukumance game da harin daga hukumomi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp