Benin ta zargi jami'an gwamnatin Nijar da shiga wajen loda danyen man kasar ta barauniyar hanya.

Hukumomin Bénin sun zargi jami'an gwamnatin Nijar da suka tsare da shiga wajen loda danyen man Nijar ta barauniyar hanya


Babban gata mai shari'ar kasar Bénin ne a cikin wata takarda da ya fitar ya ce tawagar jami'an gwamnatin Nijar din su biyar karkashin jagorancin mataimakiyar daraktan kamfanin WAPCO ta shiga cibiyar loda danyen man na Nijar ne da ke Semé Kpodji ta barauniyar hanya ba tare da an tantance su ba don haka ne suka kama su


Tuni dai a nasu bangare hukumomin na Nijar suka dauki matakin dakatar da tura danyen man har sai hukumomin Bénin din sun jami'an nasu

Post a Comment

Previous Post Next Post