Tawagar wasu 'yan Majalissar wakilai a Najeriya sun tayar da wani sabon batu na buƙatar a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyara, yadda za'a mayar da shugabancin kasar tsarin karba-karba a tsakanin yankuna shida na ƙasar.
Waɗannan 'yan Majalissa sun kuma buƙaci idan aka tashi yin gyaran fuskar na tsarin mulkin, a mayar da wa'adin shugaban ƙasa da na gwamnoni shekara shida sau ɗaya tal, sabili da hakan zai taimaka gãya wurin rage kashe kudin gudanar da harkokin mulki a ƙasar.