Bola Tinubu ya nada shugaban hukumar kula da ayyukan 'yan sanda


Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar da nadin DIG Hashimu Argungu (Rtd) a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan 'yan sanda wato 'Police Service Commission'.

Kazalika, shugaban kasar ya kuma amince da nadin Chief Onyemuche Nnamani a matsayin Sakataren hukumar da kuma DIG Taiwo Lukanu (Rtd) a matsayin mamba a hukumar.

Bugu da kari, shugaban kasar ya kuma amince da nadin Mohammed Seidu a matsayin shugaban asusun tallafa wa 'yan sanda na 'Police Trust Fund'.

Wadannan nade-nade na a cikin wata sanarwa daga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Mr Ajuri Ngelale da DCL Hausa ta samu kwafi.

Post a Comment

Previous Post Next Post