A ƙoƙarin ganin an karɓe mulkin Najeriya daga shugaba Tinubu, wata tawagar da ta kira kanta ta 'yan kishin Najeriya wato "The Patriots" a turance, ta tsara yadda zata haɗa tsofaffin 'yan takarar shugabancin Najeriya na manyan jam'iyun adawa uku a ƙasar su yi wa 'yan Najeriya bayani a ranar bukin dimakuradiyya a Legas, jihar shugaba Tinubun.
Duk da dai wannan ba shine karon farko ba da 'yan takarar Atiku Abubakar na PDP, da Kwankwaso na NNPP da kuma Peter Obi na Leba party ke hada hanya a siyasance amma daga bisani kowa ya kama tasa, a wannan karon, wannan tawagar ta 'yan kishin Najeriya da alamu tana ƙoƙarin jifar tsuntsu biyu ne da dutse guda, saboda a sanarwar da ta fitar ta hannun Farfesa Anthony Kila, ta ce a wannan taro za kuma su nemi a samar da kundin tsarin mulki da kowa zai more shi a Najeriya.
Wannan sanarwa ta nuna cewa a babban taron na ƙasa kan bikin dimakuradiyyar Najeriya, za'a karkata sosai kan batun samar da kundin tsarin mulkin Nijeriya da kowa zai amfana a ƙasar, haka ne ma ya sa aka yi wa taron lakabi da "Samar da makoma mai ma'ana ga 'yan Najeriya ta hanayar samar da tsarin mulki irin na jama'a" inji kwamitin tsare-tsaren wannan taro.
A baya-bayanan dai Atiku Abubakar da Peter Obi sun gãna tare da tattaunawa kan yadda za su haɗa karfi wurin karɓe mulki daga shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, saidai a iya cewa idan dukkanin tsofin 'yan takarar uku suka kasance a taron da za ayi ranar 12 ga wannan wata na Yuni, to shine karon farko da zasu kasance tare kan manufa guda ta siyasa tun bayan shan kaye a zaɓen shekarar 2013 na shugaban kasa da ya gabata a Najeriya.