Shaida na farko da ya baiyana a kotu kan shari'ar tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar cewa har ya yi ritaya daga aikin gwamnati a watan Mayu na shekara ta 2023 ba'a aiwatar da aikin kwangilar da aka bayar na Naira miliyan dubu ɗaya da ɗari huɗu ba a filin sauƙa da tashin jirage na jihar Katsina.
Shaidan na EFCC mai suna Azubuike Okorie, wanda tsohon Darakta ne a ma'aikatar ta sufuri lokacin da Hadi Sirikan ya ke Minista, ya tabbatar da hakan saboda a cewar sa, a lokacin da Hadi Sirika ya ke Ministan, tare da shi su ke zagayawa suna duba dukkan ayyukan kwangila da ma'aikatar sufuri ta bada.
Shaidan na EFCC ya kuma ce Kamfanin Al-Buraq aka baiwa wancan kwangila na filin jirgi da ke Katsina, amma a lokacin da suka je duba aikin tare da kwamitin sa, wannan Kamfani na Al-Buraq ya tattara kayan sa ya yi gaba ba tare da yayi wani aiki ba.
Ana zargin Hadi Sirika da hada baki da surukin sa da ma 'yar sa Fatima da wai kamfanoni wurin yin almundahana na kuɗaɗen kwangila da suka kai sama da Naira biliyan biyu.