Najeriya tana asarar biliyoyin Naira a fasa kwafrin man fetur da 'yan sumoga


Shugaban hukumar kwatsam a Najeriya Bashir Adewale Adeniyi ya baiyana cewa masu fasa kwafrin man fetur zuwa ƙasashe makwafta su na janyo wa Najeriya rashin samun kuɗin shiga saboda ƙazamar riba da su ke samu idan suka fitar da man.

Shugaban na Kwatsam ya ce yanzu sun ƙirƙiri wata runduna ta sintiri da su ka laƙa wa suna "Operations Whirlwind" wanda a yanzu haka sun yi nasarar kwace mai sama da lita dubu 150 cikin makwanni biyu daga masu fasa kwafrin, wadda kuɗin su ya kai sama da Naira miliyan ɗari, ya na mai cewa wannan ƙalilan ne daga cikin haramtacciyar kasuwanci na biliyoyin Naira da 'yan sumogan ke yi.

A yayin zantawa da yan jarida a Yola, jihar Adamawa daya daga cikin jihohi da ake fasa kwafrin man zuwa jamhuriyar Kamaru, yayi alwashin kawo ƙarshen wannan mummunar al'ada.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp