Gwamna Abba na Kano ya zargi Ganduje da sayar da makarantun Gwamnati

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yana zargin tsohuwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin jãgorancin Abdullahi Ganduje da mayar da wasu makarantun Gwamnati shaguna ta kuma sayar da wasu.

Gwamnan Kanon ya ce gwamnati da ta shude a Kano ta yi wa ɓangaren ilimi riƙon sakainar kashi saboda haka ne ya sanya shi aiyana dokar ta ɓaci a ɓangaren na ilimi a Kano.

Gwamna injiniya Abba Kabir Yusuf ya baiyan cewa zai haɗa kai da ƙungiyar malami NUT dan farfaɗo da ilimi a Kano, saboda da shi ake samar da cigaban al'umma.

Ya nuna damuwa matuƙa kan yawan yara da ke barin makaranta a Kano, ya kuma ce akwai wasu yara kusan miliyan guda da basu samu damar shiga makaranta ba.

Jihar Kano ita ce ta 18 a jerin jihohin Najeriya da suka fi cigaba ta ɓangaren ilimi mai kaso 48.9 na wadanda suka je makaranta inji hukumar kula da ilimi ta majalisar dinkin duniya UNESCO, amma kuma ita ce ta ɗaya a yawan al'umma, mai sama da mutane miliyan tara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp