Tinubu ya shiga ganawa da kwamitin karin mafi karancin albashin
Mambobin kwamitin da ke tattauna yadda za a fitar da sabon mafi karancin albashi a Nijeriya sun gana da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron na zuwa ne bayan dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki biyar da kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi na Najeriya Labour Congress, (NLC) da kungiyar kwadago, (TUC) suka yi.
Majiyar DCL Hausa ta ce kwamitin ya ziyarci shugaban na Nijeriya ne domin ya sanar da shi yadda kungiyoyin kwadago suka bukaci a yi musu kari akan N60,000 na tayin da gwamnati ta yi.
Daga cikin matsayar da aka samar har da karin da kungiyoyin kwadago suka nema na a biya ma'aikata sama da Naira Dubu Sittin a matsayin sabon mafi karancin albashi.