Tafiya Mabudin Ilmi: Abin da ya faru da ni daga Kano zuwa Yola jihar Adamawa

Direban da ya dauke mu zuwa Yola jihar Adamawa mai shegiyar gardama 'kamar makahon jaki'. Bayan motarmu ta cika a tasha ya fita za mu kama hanya ashe bai sha mai ba, yana fita tasha ya ga wani gidan man gwamnati NNPCL an bude, ga layi hada wadanda suka kwana a wurin, amma ya yanki layi daga tsakiya ya kutsa motarsa. Kan ka ce 'kobo' ya samu da ya shiga. Da ya ke masu azancin magana na cewa 'mugu shi ne ya san makwantar mugu' take tsagerun gidan man nan suka yi waje da mu duk kuwa runtsin da ke da akwai. Duk da taurin kansa, sai da ya sauka ya je da lalama da ban hakuri ya shiga layin 'yan alfarma.

Jihohi uku ne ake shiga idan za a je Yola daga Kano, idan ka cire Kano din, sai Jigawa, Bauchi da Gombe. A kan hanya na yaba kokarin gwamnatocin jihar Jigawa na yadda suka shimfida tituna masu kyau (ba laifi). Hanya mai gargada kuwa sai mutum ya shiga yankin jihar Bauchi. Daga Darazo jihar Bauchi kafin mutum ya isa Gombe, sai ka ji kamar direba ya tsaya ka tafi a kafa, (ni kadai na ji abin da na ji).

Daga Gombe titin zuwa Yola jihar Adamawa.

Akko-Dukku-Kumo-Billiri-Kaltungo kafin a isa Ngurore zuwa Numan, na ga tsaunuka manya-manya da suka zagaye yankin.

Da ka fita Kaltungo kafin Ngurore, sai kwanoni hagu da dama, kafin ka gama ta hagu ka waiga a ta dama. Ga tsauni ga hawa da sauka. Mota na kwana a irin abin da Bafulatani da ya hau keken da ba birki, yana cewa kwaneri keke, da kwana ta kiya, sai ya ce to birkel. Haka motoci ke yi a wannan hanya.

A karamar hukumar Kumo ta jihar Gombe ne za ka ga yadda maza ke fita waje su shimfida tabarma ko darduma su sha iska, haka mata ke yi. Kazalika, yadda awaki ke yawo a cikin gari haka alade ke nasa yawon. Oh! Na ga abin mamaki, ko don hakan ya saba da al'adar da na tashi cikinta? Ga noma al'ummar yankin Kumo na yi na fitar hankali (kun san idan Bakatsine ya ce haka, to yabo ne) amma wata irin hudar noma na ga ana yi kamar 'zamiyar-zakara'. Mutanen Kumo na jinjina muku. Mata a bisa babur roba-roba hada goyon biyu duk na gani a yankin Kumo ta jihar Gombe.

Kai jama'a, har sai da na tausaya wa kaina, ga bacci a idona, amma ina ido kifi ido bado, ina son in runtsa amma kuma Ina son ganin gari/hanya, tun da ban taba shiga Arewa ta gabas ba sai a wannan lokacin. Na dauka irin abin da bature ke cewa 'i have seen it all in life' ashe ban ga komai ba, sai da na ga direban da ya dauko mu ya aiki soja neman canjin 1k don ya bashi na-goro N50.Duk a cikin yankin jihar Gombe ne na an gina daki, an buga masa kwano, amma an yi bangon danga wato darni na cuci, (ban san ya suke kiransa a can ba).

Abin da na lura da shi, shi ne, akwai shingen jami'an tsaro a kan titin, kama daga sojoji, 'yan sanda, jami'an kiyaye hadurra na Road safety, na binciken ababen hawa na VIO, Civil Defense, Immigration da Kwastam, amma babu wanda bai tambayarku katin shaidar zama dan kasa. Amma wasu daga cikin fasinjojin da muke tare sun ce duk salon karbar na-goro ne.

A iya abin da idona ya gani, a halin yanzu yankin arewa maso gabas ya fi arewa maso yammacin Nijeriya zaman lafiya da kwanciyar hankli. A nan ne za ka ga gidajen da ba su wuce biyar zuwa 10 ba, sun tayar da gari, kuma su na zamansu lafiya.

Abdullahi Garba Jani
agarbajani@gmail.com
04/06/2024

1 Comments

  1. World is like a book Any one that don't travel read only one page

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp