Sojoji sun hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa a Giwa jihar Kaduna


Rahotanni daga karamar hukumar Giwa jihar Kaduna na cewa sojoji sun yi nasarar hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa a wani harin da suka kai a yankin.

Wannan harin da sojoji suka kai ta sama da kasa ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan bindigar, ciki kuwa hada wasu daga cikin jagororinsu a yankin Bula a cikin Dajin Yadi na karamar hukumar ta Giwa a jihar Kaduna.

Kamar yadda sako ya isa ga gwamnatin jihar Kaduna, an kai wannan harin ne biyo bayan wasu bayanan sirri da aka samu bayan kashe wasu jiga-jigan 'yan bindiga a kan iyakar Kaduna-Katsina.

Bayanan sirrin dai sun ce 'yan bindigar sun hadu a Dajin Yadi ne domin su kitsa yadda za su farmaki al'ummomi daban-daban na jihar. Bayan samun wannan bayani, jami'an tsaro suka kimtsa suka tunkare su yadda ya kamata, kuma suka yi nasarar yin fata-fata da su.

Bayanin hakan dai na cikin wata sanarwa daga kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan da DCL Hausa ta samu kwafi.

Post a Comment

Previous Post Next Post