'Yan bindiga sun yi mummunan ta'adi a kauyen Katsina

Wasu 'yan bindiga da ba a san adadinsu ba, sun kai hari kauyen Mai Dabino na karamar hukumar Danmusa jihar Katsina, inda suka hallaka kusan mutane 9.

Majiyar DCL Hausa ta ce da yawa daga cikin wadanda aka kashe din kone su aka yi da wuta.

Majiyar ta ce maharan sun shiga garin da yammacin Asabar har zuwa karfe 2 na daren wayewar Lahadi, inda suke harbin kan mai uwa da wabi.

Kazalika, bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce maharan sun kuma kone duk wasu manyan shaguna da ke garin, da gidaje da motoci a lokacin wannan harin.

Bugu da kari, 'yan ta'addar sun kuma sace mata da kananan yara da ya zuwa yanzu ba a san adadinsu ba.

Majiyar DCL Hausa ta ce yanzu haka da sanyin safiyar Lahadi, an fara jana'iza wadanda aka kashe a kauyen.

Mazabar Mai Dabino na daga cikin mazabu 11 na karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina da ke fama da matsalar tsaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post