Kungiyar kare hakkin Musulmi a Nijeriya ta zargi Gwamna Aliyu na jihar Sokoto da shirin tsige Sarkin Musulmi


Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta koka kan shirin da Gwamnan jihar sakkwato Ahmed Aliyu keyi na tsige sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.Babban daraktan kungiyar Farfesa Isiaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce da takun saka a kan tsige wasu sarakuna a jihar Kano.


A baya dai Gwamna Aliyu ya kori sarakunan gargajiya 15 bisa zargin su da wasu laifuka.


A cikin sanarwar, Akintola ya ce musulmin Nijeriya sun ki amincewa da duk wani tunanin na yunkurin tsige sarkin musulmin.

Post a Comment

Previous Post Next Post