Mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa ta rasu

Mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa ta rasu 

Mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa kashim shettima Maryam Albishir mai shekaru 69, ta rasu a Kano da yammacin ranar Lahadi bayan doguwar jinya da tayi fama da ita.


A wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Mista Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu ta bayyana rasuwar tata.


Za a yi jana'izar Hajiya Maryam, mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Shettima da yammacin ranar Litinin a Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp