Peter Obi yayi kira da al'umma su hada hannu wajen kawo gyara a Nijeriya

Peter Obi yayi kira da al'umma su hada hannu wajen kawo gyara a Nijeriya

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi,ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su hada kai domin kawo sauyi ga al’umma.


Ya kuma yi kira da  shugabanni su dauki mataki domin magance halin da kamfanoni da dama ke ficewa daga Nijeriya, inda ya bayyana cewa hakan yana jawo asarar da aka yi kiyasin Naira tiriliyan 95 cikin shekaru biyar da suka gabata.


Obi, a cikin wata sanarwa daya fitar a shafin sa na X, ya bayyana ficewar manyan kamfanoni goma a cikin shekarar da ta gabata kadai, wadanda suka hada da GlaxoSmithKline, Equinor, Sanofi-Aventis, Bolt Food, Procter & Gamble, Jumia Food, PZ Cussons, Kimberly-Clark, da Diageo.


Yace ya zama dole a magance ficewar da wasu kamfanoni daga Nijeriya ke yi a wannan lokacin domin yana janyo asara ga al'ummar kasar baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post