Dole ne mu kare sarkin musulmi- Kashim Shettima

Dole ne mu kare sarkin musulmi- Kashim Shettima.


Mataimakin Shugaban ƙasar ya faɗi hakan ne a jihar Katsina a wajen kaddamar da taron inganta tsaro da kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta shirya.


Taron ya samu halartar Gwamnonin shiyyar guda 7 da sarakunan Katsina, Daura, Zazzau, Kazaure da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammd Sa'ad Abubakar III.


Shettima yace cikin dukkan al'amuran ci gaba a kasar nan, mai martaba sarkin musulmi, anayin komi dashi don haka yazama wajibi muyi godiya ga dukan iyayenmu na sarakuna a kasar nan.


Ya kuma mika sako ga mataimakin gwamnan Sakkwato wanda ya wakilci gwamnan, inda yace sarkin musulmi bawai sarkin musulmi ne kawai ba, ya fi wannan matsayin a wajen mu domin yana wakiltar al'umma ne gaba daya a kasar nan don haka yana bukatar kariya,  don ci gaban al’ummarmu,


Ya bayyana haka ne bayan babban daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Isiaq Akintola, ya koka da cewa gwamnatin Sokoto na shirin tsige sarkin musulmin.


A baya dai gwamna Ahmed Aliyu ya kori sarakunan gargajiya 15 bisa wasu laifuka.

Post a Comment

Previous Post Next Post