Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya da su guji shan da ake hadawa a gida kamar, Kunu da Zobo
Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya da su guji shan abin sha da ake hadawa a cikin gida irin su kunu, zobo da fura domin gujewa yaduwar cutar kwalera.
Karamin Ministan Muhalli, Iziaq Salako ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Salako ya ce matakan kariya ga kamuwa da cutar shine tsaftace muhallinsu a ko da yaushe da dena zubar da shara musamman a wuraren ba a kebe ba.
Yace amfani da ruwa mai tsafta na da matukar muhimmanci ga lafiyar al'umma musamman idan ansamu masu tafasa ruwan kafin amfani dashi
A guji shan abubuwan da aka shirya a gida kamar su kunu, zobo, fura da nono, koko, ruwan ‘ya’yan itace da sauransu sai dai an tabbatar anyi cikin tsafta da aminci.
Ya kuma yi kira ga Jihohi da Kananan Hukumomi da su kara sanya ido kan lafiyar muhalli a wuraren da ake sayar da abinci da abin sha a fadin kasar nan.
Waɗannan wuraren sun haɗa da kasuwanni, gareji, makarantu, gidajen abinci, filin wasa, wuraren ibada da na wasanni.