Rundunar 'yan sandan kano sun tura karin jami'ai zuwa manyan fadojin jihar biyu

 Rundunar 'yan sandan kano sun tura karin jami'ai zuwa manyan fadoji 2 a Kano

Rundunar ‘yan sandan ta tura karin jami’an tsaro zuwa manyan fadadoji guda biyu da ke dauke da sarakunan da ke bangarorin biyu


Tsohon kwamishinan ‘yan sandan Kano, AIG Usaini Gumel ne ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ta wayar tarho.


Gumel ya ce, “An tura jami’ai da kayan aiki domin tunkarar duk wani abin da ba a yi tsammani ba a yankunan da aka gano a cikin garin, don haka hukumar .'yan sanda za ta cigaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar.


Ya bayyana cewa tura sojojin na da nufin hana barazanar tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya har sai an samu sakamakon rikicin na masarautar.


AIG Gumel ya ce rundunar ta kara karfafa shirinta na tura jami’anta domin tabbatar da ingantaccen tsaro da zaman lafiya a jihar.


“An baza jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a fadar Kofar Kudu, gidan sarki Malam Mohammadu Sunusi, da kuma fadar Nasarawa Mimi, gidan sarki Aminu Bayero,” inji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp