Sabuwar kungiyar tawaye a Nijar tace ta ita ce ta yi garkuwa da kantoman Bilma

Sabuwar kungiyar tawaye a Nijar ta FPJ ta yi ikirarin cewa ita ce ta yi garkuwa da Kantoman Bilma nan da mukarabbansa

A cikin wani sako ta shafukan sada zumunta, sabuwar kungiyar tawaye ta Front Patriotique pour la Justice ko FPJ a takaice ta ce ita ce ke da alhakin kame shugaban karamar hukumar Bilma da ke cikin jihar Agadez Commandant Amadou TORDA tare da mukarabban sa 4 ciki har da babban jami'in tsaron Gendarmerie na yankin Bilma


Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Mahamat Tori ta zargi hukumomin mulkin sojan Nijar na CNSP da jefa kasar cikin yanayin kama karya da rashin adalci


A ranar Juma'ar da ta gabata ne 15 ga watan Yunin nan tawagar Kantoman na Bilma a yayin da take kan hanyar ta ta dawowa daga Dirkou bayan halartar wani taron adda'o'in zaman lafiya da kungiyar farar hula ta M62 ta shirya ta fuskanci harin kwantan baunar 'yan tawayen inda suka budewa tawagar huta nan take lamarin da ya kai ga yin garkuwa da su

Post a Comment

Previous Post Next Post