Kotu ta sake saka ranar sauraren karar neman sauke Ganduje daga shugabancin APC


Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta saka ranar 5 ga watan Yuli, 2024 a matsayin ranar da za a cigaba da sauraren karar da ke neman a sauke Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC na kasa.

A karar da kungiyoyin jam'iyyar APC na Arewa ta Tsakiyar Nijeriya suka shigar su na neman da a sauke Gandujen daga shugabancin jam'iyyar a mayar da mukamin a yankin nasu.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Saleh Zazzaga ya ce suna bukatar kotu ta turasasa wa Abdullahi Ganduje ya daina kiran kansa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa.


Post a Comment

Previous Post Next Post