Farashin masara na cigaba da jijjiga aljihun talakan Nijeriya


Farashin buhun masara mai cin tiya 40 na cigaba tashi a wasu kasuwannin sassan Nijeriya, inda a kasuwar Karamar Hukumar Gombi da ke jihar Adamawa da aka sai da N100-102,000, yayin da a makon jiya aka saya N87,000.

A jihar Lagos da ke yankin Kudancin Kasar Najeriya an sayi Buhunta N100,000 a makon karshe na watan Yunin 2024, haka nan batun yake a makon jiya.

To a kasuwar Mai'adua jihar Katsina dai farashin masara bai sauya zani ba ,an sayi buhunta N95,000 a makon jiya, hakan kuwa aka sai da a wannan mako.

Sai dai a kasuwar Dandume jihar Katsina an sayi buhun masara kan kudi N85-88,000 a makon nan.

N85,000 aka sayi buhun masara a kasuwar Dawanau da ke jihar a wannan makon da ke shirin kare wa, haka dai aka sai da a wancan satin.

Sai kuma kasuwar Giwa jihar Kaduna, inda aka sayi buhun masara N88,000 a satin nan, yayin da aka saya N86,000 a makon da ya gabata.

Sai kuma ɓangaren shinkafar Hausa da ta fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna da aka saya N155,000 a satin nan, amma a makon jiya N150,000 aka sayi buhun Shinkafar,
An samu ƙarin N5000 kenan a sati guda.

 A Mai'adua jihar Katsina an sayi shinkafar N14500,00 a makon nan, haka nan aka sai da a satin da ya gabata.

To a kasuwannin jihohin Adamawa da Lagos an sayar da buhun shinkafa 'Yar gida N150,000 a satin nan, farashin dai bai sauya zani ba da na makon jiya.

Sai kasuwar Dandume jihar Katsina, an sayi buhunta N140-170,000 a satin nan.

Ita ma dai kasuwar Karamar Hukumar Girie N150,000 aka saya a makonni biyu da suka shude, haka kuma yake a wannan makon.

Shinkafar waje kuma ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da ake sayar wa N67,500.

Sai dai a kasuwar Giwa jihar Kaduna N88,000 ake sai da buhun a makon nan, yayin da a makon jiya aka saya N86,000.

Sai kasuwar Dawanau jihar Kano aka saya N87,000, bayan da a makon jiya aka saya N85,000, an samu karin N2,000 kenan.

To a kasuwar Dandume jihar Katsina an sayi buhun Shinkafar waje N78,000 a satin nan.

Sai kuma kasuwar Mai'adua jihar Katsinan aka sayi buhunta kan kudi N81,500, inda a makon jiya kuma aka saya N81,000.

A kasuwar Mile 12 International Market Lagos ana sai da buhun N80,000 a satin nan, yayin da a makon da ya wuce aka saya N83,000.

To idan muka leka bangaren farin wake ma dai farashin na ci gaba da tashi a sassan kasuwannin kasar musamman kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a kudancin kasar.

Inda aka sayi buhunta N250,000 cif a kasuwar Mile 12 International Market Lagos a makon nan, yayin da a satin da ya gabata aka saya N220,000, an samu karin N30,000 a mako ɗaya kacal.

Ita ma dai Kasuwar Dandume jihar Katsina an sayi Buhun N180-190,000 a makon nan.

Sai Jihohin Kaduna da Katsina da ake sayar da buhun farin wake N175,000 a makon nan, sai dai farashin ya bambanta a makon da ya gabata da aka saya N170,000 a kasuwar Mai'adua jihar Katsina.

N165-170,000 ake sayar da buhun farin wake a kasuwar Gombi jihar Adamawa a makon da ya gabata, haka batu yake a wannan makon.
 
A kasuwar Dawanau jihar Kano N178,000 aka sayi buhun wake a satin nan, yayin da a makon jiya aka saya N175,000.

Bari mu karkare farashin kayan abinci na wannan makon da Farashin Spaghetti.

N17,000 cif ake sai da kwalin taliyar a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a wannan satin, haka farashin yake a makon jiya.

Sai Mai'adua jihar Katsina da aka sayi kwalinta kan kudi N15,500 a wannan makon, amma a makon da ya gabata N150,000 cif ne kuɗinta.

Sai dai kwalin taliyar ya fi sauki a jihar Katsina a kasuwar Dandume na jihar da ake saidawa N14,500.

An sayi kwalin Spaghetti N13,700 a kasuwar Dawanau jihar Kano a makon nan, bayan da a makon da ya shude aka saya N13,500.

Ita kuwa kasuwar Giwa jihar Kaduna,N14,000 daidai aka sayi kwalin taliyar a wannan makon,haka nan aka saya a makon daya wuce.

N13,000 ake sai da kwalinta a kasuwar Zamani da ke jiya Adamawa a satin nan,bayanda a makon jiya aka saya N14,000 cif.

DCL Hausa A'isha Usman Gebi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp