Shugaba Tinubu ya yi tuntube ya fadi a filin taro na Eagle Square


Shugaban kasar dai na kan hanyarsa ta zuwa kusa da motar da za ta dauke shi domin zagaya masu faretin murnar Ranar Dimokradiyya da ake yi a Larabar nan 12 ga Yuni, 2024 a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.

Jami'an tsaro da sauran mataimakansa na musamman dai sun zagaye sun tattare inda shugaban kasar ya yi tuntube kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

A Wani faifan bidiyo da gidan talabijin na TVC ya wallafa mai tsawon dakika 25 ya nuna yadda Shugaba Tinubu ya yi tuntuben a lokacin da ya so kamo karfen mota ya zame bai iya kamowa ba.

Shugaban kasar da ke sanye da fararen kaya da kalar hular da ya saba sanyawa, ya yi ta kokarin ya ruko karfen motar da ke kusa da shi, amma ya gaza, samar sai da ya kai kasa, yayin da mataimakansa da sauran jami'an tsaro da kai masa dauki

Post a Comment

Previous Post Next Post