Sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci hakimai da su shiga Kano don shiryen shiryen sallah

Sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci hakimai da su shigo Kano ranar asabar domin shirye-shiryen gudanar da Hawan Sallah.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi ya sanyawa hannu kuma aka turawa hakimai.


Sanarwar ta umarci hakimai da su tabbata sun Isa fadar sarkin dake gidan sarki na Nasarawa a ranar asabar mai zuwa domin gudanar da taron da za a sanar da su yadda hawan sallar zai kasance.

Takardar mai dauke da kwanan wata 10 ga watan yuni 2024, Wanda ya yi dai-dai da 4 ga watan zul-hijja 1445 bayan hijira, tace tun masarautar Kanon ta sanar da shugabannin kananan hukumomin jihar kano yadda zasu taimakawa hakiman don gudanar da bikin sallah babbar cikin lumana.

Post a Comment

Previous Post Next Post