Mahajjaciya daga jihar Borno ta haihu a wani asibiti da ke birnin Makka
Wata Hajiya 'yar shekara 30 ta haifi da namiji a wani asibitin kasar Saudiyya dake birnin Makkah.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA, mahajjaciyar ta isa dakin gaggawa na Asibitin ne bayan ta yi fama da ciwon nakuda.
Nan take jami’an agajin suka duba halin da take ciki sannan suka kaita dakin haihuwa, inda ta haifi yaron nan take.
Yayin da mahaifiyar ke samun sauki, jaririn mai suna Mohammad yana samun kulawa ta musamman, a cikin asibtin.
Kamar yadda jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito, wannan shine karo na farko da mahajjaciya ta haihu a lokacin Hajjin shekarar 2024.
A halin da ake ciki, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta NAHCON na aikin Hajjin 2024 a kasar Saudiyya, Dakta Abubakar Ismail ya tabbatar da cewa Mahajjaciyar mace ‘yar jihar Borno ce.
Ya ce kungiyar likitocin ta kasa ta samu rahoto kan ci gaban da aka samu daga kungiyar likitocin jihar Borno inda ta ce matar ta kaucewa aikin tantance lafiyar da ya wajaba a Nijeriya.