Matawalle ya bayar da gudunmawar raguna 4,860, N390m ga shugabannin APC na Zamfara

Matawalle ya bayar da gudunmawar raguna 4,860, N390m ga shugabannin APC na Zamfara

Karamin ministan tsaro,Bello Matawalle, ya bayar da gudunmawar raguna 4,860 da kuma Naira miliyan 390 ga jam’iyyar APC, shugabanni da masu ruwa da tsaki da kuma iyalai marasa galihu a Zamfara.


Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar ranar Talata.


Sanarwar tace ragunan da kuma tsabar kudi an bayar ga Iyalai musamman marasa galihu su zasu ci gajiyar shirin gabanin bikin Eid-el-Kabir na 2024.

A cewar sakataren, za ayi rabon da kamar yadda tsohon gwamnan ke yi a duk shekara a tsakanin bangarori daban-daban a fadin jihar.


Ya kara da cewa an dauki wannan matakin ne domin a taimakawa ‘ya’yan jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki da kuma sauran al'umma domin gudanar da bukukuwan Sallah Eid-el-Kabir cikin jin dadi.


Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na Jiha da kuma shugabannin jam’iyyar a matakin kananan hukumomi da kuma gundumomi a daukacin kananan hukumomi 14 na jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post