Magidan da dama a Taraba sun zabi sayan abinchi maimakon ragon layya a babbar sallah

Magidan da dama a Taraba sun zabi sayan abinchi maimakon ragon layya a babbar sallah.


Wani bincike da Daily trust tayi ya nuna cewa tashin farashin kayan abinci ya hana mazauna yankin da dama sayen ragunan layya.


Wani magi dance a yankin,Yakubu Adamu ya bayyanawa Daily Trust cewa sabanin shekarun baya da kayan abinci ke da araha, tsadar kayayyaki da ake samu a halin yanzu ya sa mazauna yankin wahalar sayen kayan abinci da na raguna.


Ya kuma kara da cewa babban abin da ke damun masu karamin karfi shi ne ciyar da iyalansu, lamarin da ya kara zama kalubale saboda tsadar rayuwa.


Saidu Lawal, wani dillali a kasuwar sayar da raguna a ta Jalingo, ya koka da rashin sayar da ragunan duk da kokarin jawo hankalin masu saye. 


Ya kara da cewa yayin da wasu mazauna garin suka zabi kananan raguna masu saukin rahusa, wasu mawadata ne kawai za su iya siyan manyan ragunan masu tsada.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp