Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da 'yan bindiga suka kai a Katsina


Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da kakkausar murya ya yi Allah-wadai da harin da 'yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Kankara da Dutsinma a jihar Katsina.

Da yake bayyana wannan sabon harin da cewa abin takaici ne, shugaban kasar ya tabbatar da cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a da kuma karya lagon masu aikata ta'addanci a sassan kasar.

Shugaban kasar ya umurci jami'an tsaro da su yi dukkanin mai yiwuwa don bi ma wadanda aka halaka hakkinsu ta hanyar yin maganin wadanda suka yi wannan aika-aikar.

Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyya ga gwamnatin jihar Katsina, iyalai da 'yan'uwan wadanda harin ta'addancin ya rutsa da su, sannan ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mr Ajuri Ngelale, wanda shi ne Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da DCL Hausa ta samu kwafi.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp