NLC ta bukaci gwamnati ta amince da N250,000 a matsayin mafi karancin albashin

 NLC ta bukaci gwamnati ta amince da N250,000 a matsayin mafi karancin albashin Kungiyar kwadago ta NLC a Nijeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta amince da N250,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin sabanin N494,000 da ta bukata a farko.


An gudanar da taro domin samun matsaya tsakanin wakilan gwamnatin Nijeriya da kuma na kungiyoyin kwadago ta yadda za a cimma matsaya daya.


Sai dai wakilan gwamnati a yayin taron sun yi wa kungiyoyin kwadago karin N2,000 inda suka bukaci su amince da N62,000 a matsayin sabon albashin.


Post a Comment

Previous Post Next Post