NLC da TUC sun janye yajin aiki a Nijeriya
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a Nijeriya sun sanar da janye yajin aikin da suka fara a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar ta TUC Festus Osifo ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja bayan wani taron hadin gwiwa na majalisar zartarwa na kasa na hadin gwiwa na kungiyar.
Za a fitar da sanarwar nan ba da jimawa ba , in ji shugaban kwadagon.
A ranar Litinin ne kungiyoyin biyu suka tsunduma yajin aiki saboda korafe - korafensu kan karin kukldin wutar lantarki da kuma rashin cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi.