Ma'aikatar kwadago a Nijeriya ta bukaci NLC su janye yajin aiki
Ministar kwadago da samar da ayyukan yi a Nijeriya Nkeiruka Onyejeocha, ta yi kira ga kungiyoyin kwadago da su dakatar da yajin aikin da suke yi domin yana gurgunta harkokin tattalin arziki a fadin kasar
.
Onyejeocha ta ce Gwamnatin Tarayya ba ita kadai ke da alhakin yanke hukunci kan kayyade nawa zai zama sabon mafi karancin albashi ba saboda ya zama dole a ji ta bakin gwamnatocin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu.
A cewarta, har yanzu wasu gwamnatocin jihohin ba su iya biyan mafi karancin albashi na ₦30,000 da aka amince da shi a shekarar 2019 ba, ina ga sabuwar bukatar NLC na a mayar da mafi karancin albashin ya koma N494,000