Ba mu janye yajin aiki ba - NLC
Kungiyar kwadago ta NLC a Nijeriya ta ce har yanzu yajin aikin da suke gabatarwa yana nan ba a kai ga kawo karshensa ba.
Kungiyar ta bayyana hakan a cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na X a safiyar ranar Talata.
kungiyar ta ce tana kan tattaunawa da dukkanin sassanta domin yanke shawara kan matakin karshe.