An sace lakcarorin jami'ar FUDMA jihar Katsina

Wasu bayanai da DCL Hausa ta samu daga jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma jihar Katsina, na cewa 'yan bindiga sun sace tare da garkuwa da lakcarorin jami'ar guda biyu.

Bayanan sun ce 'yan bindigar sun sace Prof Richard Kyaram da dansa mai suna Solomon a gidan da suke zaune a Unguwar GRA cikin garin Dutsinma, jihar Katsina.

Bugu da kari, 'yan bindigar sun kuma sace karin wani malamin jami'ar da aka bayyana sunansa da Dr. Hamza duk a cikin Unguwar ta GRA, Dutsinma.

Lamarin kamar yadda DCL Hausa ta samu labari, ya faru ne da sanyin safiyar Litinin da misalin karfe 1am. Bayanai sun ce 'yan bindigar da dauke da muggan makamai sun shiga Unguwar ta GRA suna harbin kan mai uwa da wabi, su na bi gida-gida kamar yadda majiyar DCL Hausa ta shaida mata.

Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin babu sahihin bayanin sashe wato 'department da wadannan lakcarori suke a jami'ar ta FUDMA. Sannan babu cikakken bayanin ko wadanda suka sace su sun kira don neman kudin fansa ko a'a. Hakan ta faru ne ta dalilin rashin samun bayani daga sashen hulda da jama'a na jami'ar, bayan da aka buga wayar jami'in hulda da jama'a na jami'ar Malam Habib Umar Aminu, ba ya kusa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq ma ba ya kusa da wayarsa a lokacin da DCL Hausa ta tuntube shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post