Shugaba Tiani ya ki karbar ministan ma'adanan kasar Bénin


A cikin wata ganawa ce da ya yi da manema labarai jim kadan bayan saukowar sa daga jirgi, ministan ma'adanan Bénin ya sanar da kin karbar bakuncinsa da shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar ABDOURAHAMANE Tiana ya yi

Ministan ya ce ya je Nijar din ne dauke da sakon na musamman na shugaba Patrice Talon ga shugaban na Nijar

Dangantaka dai na kara yin tsamin a tsakanin kasashen biyu makwabtan juna duk kuwa da kiraye kirayen da wasu 'yan kasashen suke na a kawo karshen wannan takun saka da suke cewa ba ya haifar wa da al'ummomin kasashen da mai ido

Post a Comment

Previous Post Next Post