Matashin shugaban kasar Sénégal Bassirou Diomaye Faye zai kai ziyarar aiki a kasashe biyu na sabuwar kungiyar AES

A cikin sanarwar da ofishin fadar shugaban kasar na Sénégal ya fitar an bayyana cewa shugaba Faye zai fara yada zango ne a babban birnin Bamako na kasar Mali kafin daga bisani ya isa birnin Ouagadougou na Burkina Faso inda daya bayan daya zai gana da shuwagabannin gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan kasashen da suka fice daga kungiyar ECOWAS tare da kafa tasu kungiyar ta AES da Nijar.

Rahotanni na cewa cikin batutuwan da za su tattauna har da na fitar kasashen daga kungiyar ECOWAS.

Daman a baya sabon matashin shugaban kasar na Sénégal ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa domin ya maido kasashen ukku cikin kungiyar ECOWAS.

Post a Comment

Previous Post Next Post