Jami'an tsaron Nijar sun cafke kasurgumin dan bindiga Baleri da hukumomin Nijeriya ke nema

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun sanar cewa sun yi nasarar kama kasurgumin dan ta'addar nan mai suna Baleri da hukumomin Nijeriya suka sanar cewa su na nemansa ruwa jallo.

Jami'an tsaro na rundunar nan ta musamman masu lakabin 'farautar bushiya' ne dai dake aikin kawo tsaro a jihar Maradi suka yi nasarar kama wannan dan bindiga dan asalin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Dan bindigar da ke gudanar da ayyukan sa a tsakanin kasashen na Nijar da Najeriya sojojin sun ce sun yi nasarar cabke shi ne a karamar hukumar Guidan Roumdji ta jihar Maradi a lokacin da yake tsaka da tsare-tsaren yadda za su kai hare-hare a kasashen biyu da yaran sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post