Umurnin kotuna na cin karo da juna kan takaddamar sarautar Kano

Bayan umarnin babbar kotun jihar Kano na bukatar Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya fice daga ƙaramar fãda dake Nassarawa a Kano, da kuma umarnin wata babbar kotun tarayya a Kanon da ta bukaci jami'an tsaro su fitar da Sarki Sunusi shi ma daga babbar fadar Sarkin Kano, sai ga wani umarni kuma daga babbar kotun jihar Kano har ila yau, wadda ya haramta wa jami'an tsaro aiwatar da umarnin kotun taraiyar kan sarki Sunusin.

Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu wacca ta bada wannan umarni, ta kuma haramta wa jami'an tsaron duk wani yunkuri na kama ko cin mutuncin Sarki Sunusin.

Sarki Sunusi shi da madakin Kano da makaman Kano tare da Sarkin Dawaki da kuma Sarkin Bãyi suka shigar da kara a babbar kotun ta Kano.

Kotun ta ɗage zama kan wannan batu zuwa ranar 13 ga watan Yuni.

1 Comments

  1. Allah ka taimakawa masutaimakonmu yan najeriya

    ReplyDelete
Previous Post Next Post