NDLEA sun kama mahajjata da hodar iblis a Legas

 NDLEA sun kama mahajjata da hodar iblis a Legas Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a Nijeriya sun kama mahajjata hudu masu niyya zuwa Saudiyya da hodar iblis a Legas.


Kakakin hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja. 


Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kai samame wani otal mallakin Emerald, Ladipo, Oshodi, jihar Legas, a ranar 5 ga watan Yuni inda suka cafke mahajjatan bayan samun bayyanan sirri.

Post a Comment

Previous Post Next Post