Manoma a Nijeriya sun ce cire tallafin man fetur da matsalar tsaro na kawo musu cikas

Manoma a Nijeriya sun ce cire tallafin man fetur da matsalar tsaro na kawo musu cikasManoma sun yi hasashen matsalar karancin abinci za ta iya karuwa a nan gaba, inda su kayi zargin cire tallafin man fetur da rashin tsaro sune dalilin faruwar hakan.


Manoman sun yi hasashen cewa za a samu karancin abinci a nan gaba ga ‘yan Nijeriya game da matsalar hauhawar farashin kayan abinci da ake fama da ita a kasar.


Hakan dai na faruwa ne yayin da manoman suka dora laifin cire tallafin da ya kara tsadar safarar kayan amfanin gona, da rashin tsaro da ke ci gaba da kawo cikas ga noma a matsayin wasu dalilan da suka haddasa matsalar abinci a Nijeriya.


Manoman, sun yi kira ga ‘yan kasar da sai sun tashi tsaye don kara farashin kayan abinci, ya na nuni da cewa matsalar abinci na iya ci gaba da kasancewa har zuwa watan Agusta.

Post a Comment

Previous Post Next Post