Makiyan jihar Kano ne suka hana gwamnatin Abba ta NNPP yin katabus-Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Makiyan jihar Kano ne suka hana gwamnatin Abba ta NNPP yin wani katabus cikin shekara daya da kama mulki - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zargi 'yan adawa a Kano da karkatar da gwamnati na shekara guda.


Kwankwaso ya bayyana hakanne yayin taron ayyana dokar ta baci kan ilimi a jihar Kano.

Ya ce wannan rana ce mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta baci kan ilimi, domin tun zuwan Abba a matsayin gwamnan yana aiki don za ka ga sawun sa a ko’ina a fadin jihar.

Duk da cewa tun bayan zabe ake fama da zuwa kotu har kusan shekara guda,har zuwa kotun koli,

Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu bukatar a je wata kotu,kowa ya san cewa Abba ne ya ci zabe.

Amma hakan besa ya kauda kansa wajen hidimtawa al'ummar da suka zabe shi ba kullum aiki yake ba dare ba rana domin wannan shine tsarin mu.

Post a Comment

Previous Post Next Post