Jam'iyyar APC na neman gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta-baci a jihar Rivers


Shugabancin jam'iyyar APC a jihar Rivers ya roki gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci a jihar.

Shugaban rikon jam'iyyar a jihar Mr Tony Okocha ne ya yi wannan rokon a lokacin wani taron manema labarai a Fatakwal babban birnin jihar.

Ya ce jihar Rivers na cikin halin yakin da ya lakume rayukan mutanen da ba a san adadinsu ba ya zuwa yanzu.

Gwamnatin tarayya dai na da hurumin kakaba dokar ta-baci a duk jihar da aka samu barkewar wata annoba, rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa, zazzafan fadan da ya ki karewa a tsakanin bangarori, barkewar wata cuta ko wasu abubuwan da ke kawo barazana ga tsaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp