Sauya taken kasa na daga cikin nasarorin da muka cimmawa a majalisar dokokin Nijeriya - Akpabio


Shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio ya ce da ba a sauya taken kasa a shekarar 1978 ba watakila, kasar ba ta san wani abu ta'addanci ba a halin yanzu.

A shekarar 1978 ne dai Gwamnatin soji ya wancan lokacin karkashin Olusegun Obasanjo ta daina amfani da wancan taken kasar.

Lilian Jean Williams dai ne ya rubuta wancan taken kasar da ake cewa "Nigeria We Hail Thee' a shekarar 1959.

Arise O compatriots da Pa Ben Odiasse ya rubuta ce aka cigaba da amfani da ita har sai da shugaba Tinubu ya ajiye ta ya maido da wancan tsohon taken kasar da aka ajiye a zamanin mulkin soji.

Ba tare da bata lokaci ne ba dai kudirin sauya taken kasar ya tsallake karatu na daya da na biyu a zaurukan majalisar dattawa da ta wakilan Nijeriya kuma shugaban kasa ya rattaba masa hannu.

Sanata Akpabio ya ce dawo da wancan tsohon taken kasar na daga cikin nasarorin da ya samu a jagorancin majalisa da yake yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post