Ba 'yan Nijeriya kadai ne ke fama da talauci ba, in ji Shugaba Tinubu


Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce ba 'yan kasar kadai ne ke fama da talauci ba a duniya.

Sai dai shugaban kasar ya aminta cewa 'yan kasar na cikin halin matsin rayuwa da talauci.

Amma a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa Mr Ajuri Ngelale, ta ce shugaban kasar ya sha alwashin shawo kan wadannan matsalolin da 'yan kasa ke ciki na talauci.

Daga cikin hanyoyin da ya yi alkawarin zai bi don shawo kan matsalolin hada kakkabe ayyukan ta'addanci don manoma su koma gona don noma abin da za su ci, su sayar.

Shugaban kasar na magana ne a Lagos a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio da sauran tawaga a lokacin sa suka je yi masa barka da sallah.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp