Sai kasuwar Dandume jihar Katsina da aka sayar da Buhunta kan kuɗi ₦83-88,000 a wannan makon.
Ita kuwa kasuwar Mai'adua a jihar Katsina ₦84,000 ake sayar da buhun masara a wannan makon, haka batun yake a satin da ya gabata.
To a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna an sayi buhun Masara ₦85,000 a satin nan, yayin da a makon jiya aka saya ₦80,000, karin ₦5000 kenan cikin mako guda.
Da DCL Hausa ta yi tattaki zuwa kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ta taras da masarar ta kara ₦2000 kan kuɗinta na makon jiya da aka saya ₦80,000 daidai, amma a satin nan ₦82,000 ne kuɗin buhun ya ke a kasuwar.
An sayi buhun Masara ₦79-80,000 cif a Kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a wannan makon, hakan kuwa aka sai da makon jiya.
To bangaren Shinkafar Hausa kuwa, ta fi sauki a makon nan a kasuwar Mai'adua jihar Katsina wanda aka sai da buhunta ₦140-145,000, haka kuɗin ya ke a makon jiya.
Sai dai shinkafar ta fi tsada a kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya ₦130-155,000.
A Mai'adua jihar Katsina an sayi buhun ₦150,000 cif a satin nan, bayan da a makon da ya gabata aka sai da buhun shinkafar Hausar ₦145,000, an samu karin ₦5000 kenan a makon nan.
Sai dai kuma kuɗin buhun Shinkafar ₦150,000 daidai ne a kasuwannin jihohin Adamawa, Kano, Kaduna da Lagos a makon nan da ke mana ban kwana, amma farashin na makon jiya ya sha banban a kasuwannin, an sayi buhun ₦160,000 a kasuwar Mile 12 International Market Legos a satin da ya gabata, amma a makon nan ₦150,000 ne kuɗin buhunta, an samu sauƙin ₦10,000 kenan, haka nan batun yake a kasuwar Karamar Hukumar Girie a jihar Adamawa.
Ita kuwa Shinkafar Bature mai cin tiya 50 ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, an sayi buhun ₦75,000 a makon nan, amma a makon da ya wuce ₦67,500 ake sai da buhun shinkafa 'yar Gwamnati.
₦76,-77,000 ake sayar da buhun shinkafar waje a kasuwar Dandume jihar Katsina a satin nan.
Sai kuma kasuwar Mai'adua a jihar Katsina aka saya ₦78,000 a makon nan da ke dab da ƙarewa, amma a makon jiya ₦78-79,000 ake sayar da buhunta.
Shinkafar waje ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da aka saya ₦85,000 a makon nan, amma a makon jiya ₦87,000 ne kuɗin buhun Shinkafar.
Ita ma dai kasuwar Mile 12 International Market Legos ₦85,000 kuɗin yake a wannan makon, farashin dai bai sauya Tufafi ba da na makon jiya.
₦80,000 daidai ake sayar da buhun shinkafar waje a satin nan a kasuwar Giwa jihar Kaduna.
Farin wake ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Legos da aka saya ₦200,000 daidai a makon nan, amma a makon jiya an sayi buhun ₦185,000 a kasuwar.
A kasuwannin jihohin Kano da Kaduna an sayi buhun farin wake ₦170,000 daidai a makon nan,amma farashin wake a jihohin ya bambanta a makon jiya,₦165,000 aka sai da buhun a kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon jiya, yayin da aka sayi buhun ₦155,000 a kasuwar Dawanau Kano a makon jiyan.
A kasuwar karamar hukumar Gombi an sai da buhun farin wake ₦160,000 a makon da ya shude, yayin da a wannan makon aka saya ₦150-160,000.
To a kasuwar Dandume jihar Katsina ₦160,000 har zuwa ₦180,000 ake sai da buhun farin wake a satin nan da ke dab da ƙarewa.
Sai kuma kasuwar Mai'adua jihar Katsina da aka saya ₦165,000 a wannan makon, inda a makon da ya gabata aka sayar kan kuɗi ₦164,000, an samu sassaucin dubu guda kenan a makon nan.
To bari kammala farashin kayan abincin na wannan satin da kuɗin kwalin taliya.
Kwalin taliyar dai ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ake saidawa ₦16,000 cif a makon nan, yayin da a makon jiya aka sayar da kwalin ₦18,000 daidai, an samu canjin dubu 2 kenan a sati guda.
To a kasuwar Mai'adua jihar Katsina an sayi kwalin taliyar ₦15,500 a makon nan,amma a makon jiya ₦15,300 kuɗin ya ke a kasuwar.
Sai kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya ₦14,000 cif a satin nan.
To a kasuwar Giwa jihar Kaduna ma dai farashin kwalin taliyar ₦14,000 a wannan makon, haka farashin ya ke a makon jiya.
₦13,500 ne ake sayar da kwalin taliya a kasuwar Dawanau jihar Kano a makon nan,bayan da a makon daya shude aka sayar kan kuɗi ₦13,000 cif.
Ita ma dai kasuwar Zamani dake jihar Adamawa ₦13,000 daidai ake sayar da Taliyar Spaghetti a makon nan,haka batun yake a makon daya gabata.
DCL HAUSA A'isha Usman Gebi.