Hisbah ta kama ɗan jarida a Katsina




Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta kama ɗan jarida Jamilu Mabai, wakilin gidan talabijin na Trust Tv a jihar Katsina.


Rahotannin da DCL Hausa ta samu sun nuna cewa hukumar ta Hisbah ta nemi dan jaridar ruwa a jallo sakamakon wani rubutu da ya yi a kafar sadarwa ta Facebook, wanda yake da alaƙa da zargin cin mutuncin hukumar da shugabanta

An kama Mabai ne a wannan Talata bayan da ya je hukumar da niyyar haɗa rahoto na zargin da ake ma hukumar na harbe wani dattijo mai sana'ar faci da bindiga, wanda hakan ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp