Ƙungiyar FPL ta yi barazanar kai hare-hare a wasu wuraren hakar man fetur a Nijar



Sabuwar kungiyar tawayen nan ta Nijar Front Patriote de Libération (FPL) ta yi barazanar fara kaddamar da hare hare a wasu wuraren hakar man fetur a ƙasar 

A cikin wata sanarwa ce da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban ta a ranar 13 ga watan Mayun nan, sabuwar kungiyar tawayen ta bayyana cewa bayan cikar wa'adin mako gudan da ta bada na soke yarjejeniyar bashin kudi nan har milyan 400 na dalar Amurka da kasar China ta ba hukumomin mulkin sojan Nijar ba tare da an soke ba ta yi kira ga 'yan Nijar da ma 'yan kasashen ketare wadanda ba su ji ba su gani ba da su gaggauta barin wuraren da ake haka da sarrafa man fetur 

Kungiyar ta zana wasu wuraren da ta ce daga yanzu su ne wuraren da za ta fara kaddamar da ayyukan ta

Cikin wuraren da kungiyar ta zano har da kamfanin matatar mai ta SORAZ da ke jihar Damagaram da dukkan wasu wuraren hako man na Agadem da ke cikin jihar Diffa

Kungiyar ta ce za ta janye daga wannan matsaya ta ta ne kawai idan har an maido kasar ta farkin dimokaradiyya da kundun tsarin mulkin

Kungiyar ta FPL ta ce manufarta shi ne ta hana satar man fetur din Nijar da wasu tsiraru suke yi don arzuta danginsu tare saka al'ummar kasar cikin mawuyacin hali

A karshe kungiyar ta ce ta shirya kirkiro hanyoyin da za su bada damar rabon arzikin man fetur cikin adalci domin gudanar da ayyukan masu muhummanci don amfanin al'ummar Nijar

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp