Mahamadou Issoufou ya maka tsohon jakadan Faransa a Nijar kotu

Mahamadou Issoufou


Tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya maka tsohon jakadan Faransa a Nijar Sylvain Itté a gaban kotu bisa zarginsa da bata masa suna

Tsohon jakadan Faransa dai a Nijar ya zargi tsohon shugaban kasar Issoufou Mahamadou da hannu a cikin juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin bara da ya yi awan gaba da kujerar aminin sa Bazoum Mohamed

Tsohon shugaban kasar ya shigar da wannan kara ne a gaban babban kotun birnin Yamai

Post a Comment

Previous Post Next Post