Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da wani kamfen na inganta ilimi da bunkasar fasaha da daidaiton jinsi.
Gangamin da aka yi wa lakabi da, "duk daya muke" wato #WeAreEqual, wani shiri ne na kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka OAFLAD.
An kaddamar da gangamin a kasashen Nahiyar Afirka 15 a fannoni daban-daban, inda aka mai da hankali kan kiwon lafiya, ilimi, karfafa tattalin arziki, da yaki da cin zarafin mata.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da gangamin da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Shugaba Tinubu ya jinjina wa kudurin matan shugabannin kasashen Afirka, a matsayinsu na mambobin kungiyar OAFLAD, na inganta daidaiton jinsi tare da takaita bambancin jinsi a fadin nahiyar.
Category
Labarai